IQNA

Taron Tunawa Da Shahaar Ima Hussain A Kenya

23:43 - September 15, 2018
Lambar Labari: 3482986
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da zaman makokin shahadar Imam Hussain (AS) a kasar Kenya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an fara gudanar da zaman makokin shahadar Imam Hussain (AS) a kasar Kenya wanda mabiya mazhabar ahlul bait suke gudanarwa a kowace shekara a daidai irin wannan lokaci.

Sheikh Abduljalil dan kasar Amurka wanda dan asalin kasar Ghana ne da ya kammala karatunsa a Hauzar Qom ta kasar Iran shi ne babban bako mai gabatar da jawabi.

Ana gudanar da wadannan taruka a birananen Mumbasa, Nakuro, Kamu, Mihanho, Sagana, da kuma masallatan biranan Ruwaita, Gashiya da sauransu.

A shekarun baya a birnin Nairobi ne kawai ake gudanar da irin wadannan taruka na tunawa da shahadar Imam Hussain (AS) a kasar Kenya, daga ranar farko har zuwa goma sha uku ga Muharram.

3747008

 

 

 

 

 

captcha