IQNA

An Hana ‘Yan Kasar Yemen Yin Karatu Makarantun Gwamnati A Saudiyya

22:36 - September 08, 2018
Lambar Labari: 3482965
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan Saudiyya sun hana ‘yan kasa Yemen da suke zaune a kasar yin karatu a makarantun gwamnati.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Akhir Akbar cewa, ma’aikatar ilimi ta kasar Saudiyya ta sanar da cewa, ‘yan kasashen Yemen da Syria da suke zaun a kasar da suke gudun hijira, ba su da hakkin yin karatu a makarantun gwamnati.

Bayanin ya ce a halin yanzu gundumar Jidda ta fara aiwatar da wannan umarni, inda ta sanar da makarantun da suke cikin lardin cewa, an dakatar da duk wasu dalibai ‘yan Yemen da Syria da suke karatu a makarantun gwamnatin kasar.

Gwamnatin kasar Saudiyya dai ita ce take taka gagarumar rawa wajen yake-yaken da suke faruwa a kasashen Yemen da Syria, kuma wannan mataki da ta dauka ya yi hannun riga ga ka’idoji na majalisa dinkin duniya  akan mutanen da suka yi gudun hijira saboda yaki.

3744649

 

 

captcha