IQNA

Adadin Shahidan Boren Komawa Gida Na Falastinawa Ya Kai 132

23:46 - June 24, 2018
Lambar Labari: 3482785
Bangaren kasa da kasa, a ci gaba da kisan kiyashin da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi kan Falastinawa a watannin baya-bayan nan mutane 132 ne suka yi shahada.

 

Kamfanin dillancin labaran anatoly ya bayar da rahotn cewa, sakamkon kisan kiyashin da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi kan Falastinawa a zanga-zanga mai taken hakkin komawa gida, mutane 132 ne suka yi shahada a yankin zirin Gaza da sauran yankuna.

Haramtacciyar gwamnatin yahudawan tana yin amfani da wannan damar wajen kashewa tare da jikkata dubban falastinawa a Gaza da sauran yankuna.

A jiya Juma’a wani matashi dan shekaru ashirin da tara ya yi shahada a Gaza, bayan da sojojin yahudawan sahyuniya suka harbe shi.

3725078

 

 

 

 

captcha