IQNA

Yaki Ya Hana Aiwatar Da Wasu Al’adu A Lokacin Idi A Yemen

23:34 - June 16, 2018
Lambar Labari: 3482765
Bangaen kasa da kasa sakamakon yakin da aka kalafa a al’ummar kasar Yemen wasu daga cikin al’adunsu a  lokacin salla ba za su yiwu ba.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai Quds ya bayar da rahoton cewa, al’adar Awadah da ake yi a emen sakamakon yakin da ‘yan mamaya suka fara kaddamarwa  akan kasar tun 2015 hakan yasa ala tilas aka daina wannan al’ada.

Al’adar Awadah wata al’ada ce ta bayar da barka da salla ga kananan yara a ranar sallah da kuma dangi da mata, domin murna salla, amma sakamakon hareharen ‘yan mamaya an dakatar da hakan.

Tun a cikin 2015 masarautar jikokin saud ta fara kaddama da hare-hare kan al’ummar kasar Yemen tare da taimaon kasashen yammacin turai da kuma yahudawa, da nufin mamaye kasar da kuma kafa mulkin mulukiyya na gidan sarautar jikokin Saud, abin da al’ummar kasar Yemen suka ki amincewa da shi.

3723059

 

 

 

 

 

 

captcha