IQNA

Muftin Quds Ya Yi Gargadi Dangane Da Yada Wani Kur'ani Mai Matsala A Bugunsa

22:46 - March 19, 2018
Lambar Labari: 3482488
Bangaren kasa da kasa, babban mai bayar da fatawa a Palastinu ya yi gargadi dangane da amfani da wani kur'ani da aka buga da kura-kurai.

 

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ramallah cewa, Sheikh Muhmamad Hussain babban malami mai bayar da fatawa a Palastinu ya yi gargadi dangane da amfani da wani kur'ani da aka buga da ke dauke da kura-kurai a cikin bugun nasa.

Malamin ya ce an buga kur'anin nea  cikin fararen takardu, inda kuma aka samu kura-kurai wajen tsara shafukansa, wanda hakan ya sabawa tsarin kur'ani.

Ya ce wadanda suke da kur'anin to su kokarta su kawo shi ga babban ofishin bayar da fatawa na Quds ko kuma sauran ransansa da ke cikin yankunan Palastinu domin tara su wuri guda.

Cibiyar buga littafai ta Daru Taufikiyya ce ta buga wannan kwafin kur'ani bayan samun izini a cikin watan mayun 2015 daga cibiyar Azhar.

3701214

 

 

 

 

captcha