IQNA

Masallatai Ba Za Su Tsoma Baki A Cikin Hakokin Zaben Kasar Ba

22:38 - March 12, 2018
Lambar Labari: 3482470
Bangaren kasa da kasa, ministan ma’ikatar harkokin addini kasar Masar ya ce masallatai ba za su saka baki cikin harkar zaben kasar ba.

Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almisri alyaum cewa, Muhammad Mukhtar Juma’a ministan ma’ikatar harkokin adini kasar Masar ya ce masallatai ba za su saka baki cikin harkar zaben shugaban kasa da za a gudanar Masar ba.

Ya ce sauran cibiyoyin addini da suka hada da makarantu da sauransu ba su fito su goyi bayan wani bangare ba, amma kowane mutum yana da zabin a kan kansa.

Haka nan kuma ya kirayi matasan kasar da su yi hattara matuka kada su bari a yi amfani da su wajen cimma manufofi na siyasa da za su kawo yamutsi a kasar.

Nan da makonni biyu masu zuwa ne za a gudana da zaben shugaban kasa a  kasar Masar, a daidai lokacin da gwamnatin kasa ke kokarin ganin ta murkuse duk wani da zai zama barazana ga Sisi a zaben.

3699018

 

 

 

captcha