IQNA

Sallah A Gaban White House Domin Nuna Rashin Amincewa Da Kudirin Trump

19:58 - December 09, 2017
Lambar Labari: 3482183
Bangaren kasa da kasa, daruruwan musulmi ne suka gudanar da salla a gaban fadar white house domin nuna rashin amincewa da kudirin Trump a kan birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin world News cewa, a jiya daruruwan msuulmi ne suka gudanar da salla a gaban fadar white house domin nuna rashin amincewa da kudirin Trump a kan birnin Quds mai alfarma, inda ya ayyana shia  matsayin fadar mulkin yahudawa.

Bayanin ya ci gaba da cewa, msuulmin sun gudanar da wannan gangami ne tare da wasu daga cikin al'ummomin Amurka wadanda ba musulmi ba ne.

Babbar manufar gudanar da wannan gangamin dai shi ne nuna wa Trump cewa abin da ya yi ya tabka babban kure, domin kuwa babu wani daga cikin shugabannin Amurka da ya taba jefa kansa cikin wannan matsala.

Kasashen duniya da suka hada har da wadanda suke dasawa da Amurka duk sun mara ma Trum baya kan kudirin nasa.

3670633

 

captcha