Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, Cibiyar labarai ta Palasdinawa ta ambaci cewa dukkan palasdinawa ne suka fito kan titunan yammacin kogin jordan da yankin Gaza domin nuna kin amincewarsu da matsayar shugaban kasar Amurka na daukar Kudus babban birnin haramtacciyar Kasar Isra'ila.
A garin al-Khalil da ke yammacin kogin Jordan, sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila da ke kan dawakai da kasa, sun yi amfani da albarusai akan masu Zanga-zangar tare kuma da harba hayaki mai sa hawaye.
A birbin kudus ma masu Zanga-zangar sun rika bada taken tir da matakin na Amurka tare da jaddada cewa birnin Kudus na larabawa da musulmi ne.
Sauran garuruwan yankin yammacin kogin Jordan da aka yi Zanga-zangar sun kunshi Jenin, Nablus, Tul Karam da Ramallah.
A kasashe da dama na duniya ma an gudanar da Zanga-zangar yin tir da Amukra da matakin da shugabanta ya dauka akan masallacin Kudus.